Skip to content

Labarai

Matani
Ma'ajiya

Jawabai

Matani
Ma'ajiya

Sakonni da Wasiku

Matani
Ma'ajiya

Darussa

Sharhin Hadisi

Littafa da Ayyuka

Littafa
Ra'ayoyi

Hikayoyi Da Tuna Baya

Kafin Juyi
Bayan Juyi

Sauti Da Hotuna

Hotuna
Sauti
Bidiyo
Jagora Ya Jinjina Wa Al'ummar Iran Saboda Jerin Gwanon Goyon Bayan Tsarin Musulunci Print
09/01/2010

 Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i, a wata da ya yi a safiyar yau asabar (09-01-2010) da dubun dubatan mutanen garin Qum da suka kai masa ziyara don tunawa da ranar 19 ga watan Dey (wato ranar da al'ummar garin Qum suka fito don yin Allah wadai da cin mutumcin da aka yi wa marigayi Imam Khumaini a shekarar 1356), ya bayyana gagarumar fitowar da al'ummar Iran ma'abota imani da kishin Musulunci suka yi a jerin gwanon ranar laraba (30-12-2009 don nuna nuna goyon bayansu ga tsarin Musulunci na Iran da yin Allah wadai da masu kokarin tada fitina a kasar) a matsayin abin da ke nuni da karfi na Ubangiji da kuma gagarumin yunkurin al'umma cikin tarihin juyin juya halin Musulunci. Jagoran ya ci gaba da cewa: ‘yan mulkin mallaka da kuma kungiyoyi masu adawa da addini wadanda a cikin irin yanayi na fitina suke rera taken kiyayya da wannan tsari da kuma juyin juya halin Musulunci su ne dai wadancan mutanen da shekara da shekaru suka shata daga wajen fada da (marigayi) Imam (Khumaini) da kuma juyin juya halin Musulunci sannan kuma al'umma ta hanyar fahimtar wannan lamari suka sake tabbatar da kasantuwarsu mai ayyana makoma wajen kare wannan tsari (na Musulunci) da kuma juyin juya halin Musulunci.

Yayin da yake ishara da bangarori daban-daban na gagarumin yunkurin ranar 19 ga watan Dey na shekarar 1356 (hijira shamsiyya) a garin Qum kuwa, Ayatullah Khamene'i ya bayyana cewar: Yunkurin al'ummar garin Qum a ranar 19 ga watan Dey shekaru 32 da suka gabata ya kebanta da wasu siffofi irin su basira, fahimtar yanayin da ake ciki, sanin makiyi, kokari da kuma haifar da sauyi da kuma gagarumin yunkuri cikin al'ummar Iran ne kuma har ya zuwa yanzu wadannan abubuwa sun zamanto darussa kuma ababe masu tasiri.

Jagora ya bayyana irada da kokarin mutane a matsayin ababen da suke share fagen faruwar wasu abubuwa na tarihi cikin kuwa har da abin da ya faru a ranar 19 ga watan Dey na shekarar 1356 yana mai cewa: Ranar 9 ga watan Dey (30-12-2009) na wannan shekarar ma tana daga cikin ranakun da suka shiga cikin tarihi sakamakon gagarumin yunkurin al'umma.

Yayin da yake ishara da irin yanayin da ake ciki a kasar Iran a halin yanzu kuwa Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: A irin wannan yanayi, muhimmancin wannan gagarumin yunkuri na al'umma yana da kara ninkuwa ne sannan kuma ana iya ganin ruhin wilaya da ruhin Husaini bn Ali (a.s.) a cikinsa. Haka nan kuma kamar yadda marigayi Imam a koda yaushe yake fadi ne ana iya ganin hannun karfi na Ubangiji a cikin hakan.

Ayatullah Khamene'i ya bayyana cewar ayyana abin da ya dace a yi a irin yanayi na fitina lamari ne mai wahalar yana mai ishara da irin abubuwan da masu kokarin haifar da fitina suka yi wajen fuskantar Amirul Muminin (a.s) a lokacin yakin Siffin. Jagoran ya ci gaba da cewa: A irin wancan yanayi mai cike da rudani, mai girma Ammar bn Yasir wanda ya kasance daga cikin mataimaka kuma mabiyan Imam Ali (a.s.) na kurkusa ya kasance mai shige da fice wajen bayyanar da gaskiya ga jama'a don ya tunatar da mutanen da suke kokarin zamewa da cewa babu wani bambanci tsakanin masu fada da Manzon Allah (s.a.w.a) da masu fada da Amirul Muminin (a.s) in banda cewa masu fada da Amirul Muminin (a.s) a zahiri suna da'awar riko da Musulunci da kuma goyon bayan Alkur'ani da kuma Annabi (s.a.w.a.).

Ayatullah Khamene'i ya ci gaba da cewa: Tun daga farkon nasarar juyin juya halin Musulunci sannan kuma tsawon rayuwar marigayi Imam Khumaini (r.a) a ko da yaushe Amurka, Ingila da sauran ma'abota girman kai da sauran wadanda suka ci baya na gaba ‘yan koren gwamnatocin ‘yan mulkin mallaka da kuma wadanda suka kauce wa hanya da suke cikin gida sun kasance masu fada da marigayi Imam da kuma juyin juya halin Musulunci, kuma a yanzu ma haka lamarin yake.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Tun kafin zaben shugaban kasa har zuwa yanzu Amurka da Ingila da kafafen watsa labaran yahudawan sahyoniya a ina suka kasance? Haka nan kuma ina kungiyoyin masu adawa da addini irin su jam'iyyar Tudeh, masu son tabbatar da sarauta da sauran masu adawa da juyin juya halin Musulunci da Imam suke? Shin ba su kasance karkashin inuwar wannan tuta ta fada da tsarin Musulunci ba ne? A saboda haka babu wani abin da ya sauya, hakan kuwa wata alama ce mai muhimmanci.

Ayatullah Khamene'i ya bayyana gagarumar fitowar da al'ummar Iran suka yi a ranar 30-12-2009 a matsayin wani sakamako na irin sanin ya kamatan da al'ummar Iran suke da shi da kuma fahimtar yanayin da ake ciki yana mai cewa: Ko da sau dubu aka yi sujadar godiya sakamakon wannan ni'imar lalle hakan ya kasa.

Jagoran ya bayyana kasantuwar al'umma a fage a matsayin ummul aba'isin din kare juyin juya halin Musulunci da kuma kasar Iran sannan kuma babban abin da ya sanya ma'abota girman kan duniya suke tsoron kawo wa al'ummar Iran hari. Jagoran ya ci gaba da cewa: Sabanin wasu farfagandar da wasu kafafen watsa labarai suke yadawa, babbar matsala makiya wannan al'umma ita ce basira da kishin addini da matasan wannan kasa suke da su ne.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: irin wannan kishin addini da sanin ya kamata ne ya sanya matasan yin hakuri da wasu abubuwan da suke faruwa wanda kuma haka ya kamata ya zama, amma a duk lokacin da ake bukatar kasantuwa a fage, lalle suna kasancewa a fagen.

Jagoran ya bayyana wajibcin la'akari da irin gazawar da ma'abota girman kai suka yi wajen fahimtar yanayin duniya da wannan yankin wajen yin sharhi kan abubuwan da suke faruwa a Iran yana mai cewa: Farkawar da al'ummar Iran suke da ita ta dama wa ma'abota girman kai lissafi, sannan kuma ta hanyar ihu bayan hari da kulla makirci suna ta kokari wajen ganin irin sautin basira da shirin da al'ummar Iran suke da shi ba su isa ga kunnuwan al'ummar musulmi ba don kada sauran al'ummar su ma su farka.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana irin fushin da matasa masu girma na Iran suka nuna dangane da cin mutumcin da wadansu suka yi wa masu juyayin Ashura da kuma Imam Husaini (a.s.) a matsayin wani abu da a dabi'ance zai faru yana mai cewa: Zukatan dukkanin al'umma sun sosu sakamakon wannan cin mutumci, to sai dai wajibi ne kowa ya yi taka tsantsan wajen ganin ba mu taimaka wa masu tayar da fitinan da kuma makiya ta hanyar ayyukanmu ba.

Yayin da yake ishara da kokarin da makiya suke yi wajen haifar da fitina kuwa Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: A irin wannan yanayi wajibi ne a yi gagarumin taka tsantsan sannan kuma a yi hukumci irin na ba sani ba sabo a inda hakan ya dace don hana masu kokarin tayar da fitinar cimma manufarsu.

Ayatullah Khamene'i ya kirayi cibiyoyin da abin ya shafa da su gudanar da ayyukansu ba sani ba saboda gwargwadon yadda doka ta tanadar ga wadanda suka haifar da fitinar da ta faru kamar yadda kuma ya kirayi wadanda ba su da hakki na doka da kada su tsoma bakinsu cikin lamarin.

Har ila yau kuma yayin da yake jaddada kiran Alkur'ani mai girma na gudanar da adalci da daidaito cikin hukumci kuwa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: wadansu mutane suna nuna kiyayya da kuma munanan ayyuka sannan wasu kuma suna goyon bayansu, to amma idan har ba a gudanar da lamurra yadda suka dace ba wajen fuskantar wannan lamari mai yiyuwa ne ‘yan kasashen waje su yi kokarin amfanuwa da hakan. A saboda haka wajibi ne a nesanci aiwatar da abubuwan da suka saba wa doka, a aikata komai daidai da yadda doka ta tanadar.

Yayin ya koma kan irin gagarumar fitowar da al'ummar Iran suka yi a ranar 30 ga watan Disamban 2009 (don nuna nuna goyon bayansu ga tsarin Musulunci na Iran da yin Allah wadai da masu kokarin tada fitina a kasar) kuwa Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana hakan a matsayin yanke hujja ga kowa da kowa, daga nan sai ya ce: Jami'an bangarori uku na gwamnati dai sun ga me wannan al'umma take so, a saboda haka wajibi ne su aiwatar da ayyukansu yadda ya dace wajen fuskantar lalatattu masu son tada fitina.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa makiya suna so ne su yi amfani da abubuwan da suka faru cikin ‘yan kwanakin nan wajen mayar da hannun agogon ci gaban tattalin arziki da ilimi na kasar Iran da kuma irin bayyana Jamhuriyar Musulunci ta Iran a fagagen kasa da kasa baya da kuma lalata hakan. Don haka wajibi ne jami'an gwamnati ta hanyar gudanar da ayyukansu yadda ya dace a fagen tattalin arziki, ilimi, al'adu da siyasa su yi duk abin da za su iya wajen ganin ba su cimma wannan manufa ta su ba.

Jagoran ya bayyana fitowar da al'umma suka yi a fage a matsayin mafi girman arziki da kuma garkuwa ga wannan tsari na Musulunci sannan kuma yayin da yake ishara da farfagandar da kafafen watsa labaran kasashen waje suke yi wajen nuna wannan gagarumin jerin gwano da al'ummar Iran suka yi a ranar (30-12-2009) da cewa gwamnati ce ta shirya shi ya bayyana cewar: Wadannan mutane ta hanyar yada irin wadannan farfaganda, ba tare da son ransu ba suna tabbatar da irin karfin da al'ummar Iran suke da shi ne, don kuwa babu wata gwamnati a duk fadin duniyar nan da cikin kwanaki biyu za ta iya yin wannan aiki da kuma taro gomomin miliyoyin al'umma zuwa kan tituna.

A karshen jawabin nasa Jagoran juyin juya halin Musulunci ya sake jinjinawa al'ummar Iran saboda irin basira da sanin ya kamatan da suka nuna.

 
< Prev   Next >
^